Gwamnatin jihar Kaduna tace kan matsayar ta na kwanaki hudu na ranar aiki a fadin jihar

0 29

Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da su koma aikin kwanaki hudu a kowanne mako, yayin da za a bude zango na 2 a makarantun jihar tindaga ranar 10 ga watan Janairu na shekarar 2021/2022.

Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal, ta fitar da wannan umarni a Kaduna a jiya Lahadi, cikin wata sanarwar dawowa karatun  zango na biyu na shekarar 2021/2022.

Kafin hakan dai Kamfanin Dillancin labarai na kasa NAN ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna a ranar 1 ga Disamba, 2021, ta sauya tsarin aiki zuwa kwanaki hudu a kowanne mako.

Cikin wani sako da mai bawa gwamnan jihar shawara akan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya fitar.

Ya bayyana cewa an tsara matakin ne don taimakawa wajen habaka nagartar aiki da habaka daidaiton rayuwar aiki a bangaren marantun jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: