Gwamna Aliyu Ya Ce Shan Miyagun Ƙwayoyi Ne Ke Haifar Da Yawancin Matsalolin Tsaro A Sokoto
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa kusan kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaro da ke addabar jihar na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa wannan mummunar ɗabi’a na daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar makomar matasa da ci gaban al’umma.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taron lacca da aka shirya domin tunawa da Ranar Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safarar Su Ba Bisa Ka’ida Ba ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shekarar 2026, wanda aka gudanar a Cibiyar Sultan Maccido da ke Sokoto.
Aliyu, wanda Mataimakinsa Alhaji Idris Mohammed Gobir ya wakilta, ya ce mafi yawan laifukan tashin hankali da ayyukan ‘yan bindiga suna da nasaba da amfani da miyagun ƙwayoyi.
“Kashi 80 cikin 100 na matsalolin tsaro da ke damun jihar nan na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi. Mutanen nan suna amfani da ƙwayoyi masu matuƙar illa. Mutum mai hankali ba zai kalli wani ya kashe shi ba tare da wani dalili ba,” in ji shi.
Ya ce shan miyagun ƙwayoyi na lalata iyalai, na hana matasa cimma burinsu, sannan yana ƙara yawaitar aikata laifuka tare da jefa al’umma cikin haɗarin lafiya da zamantakewa.
Gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙara ƙarfafa ayyukan ta’addanci da kungiyoyin masu aikata manyan laifuka, yana mai cewa da dama daga cikin ‘yan bindiga da masu aikata ta’asa suna aikata munanan laifukansu ne ƙarƙashin tasirin ƙwayoyi.
Ya jaddada cewa yaƙi da matsalar ba aikin hukumomin tsaro kaɗai ba ne, yana buƙatar haɗin gwiwar iyaye, malamai, shugabannin addini da na gargajiya, ƙungiyoyin farar hula, masana lafiya, shugabannin al’umma da kafafen yaɗa labarai.
Aliyu ya ce gwamnatin jihar ta kafa Ofishin Babban Mataimaki na Musamman Kan Kula da Hana Shan Miyagun Ƙwayoyi domin wayar da kai da kuma haɗa kai da masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da matsalar.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke da nufin hana shan miyagun ƙwayoyi, gyaran waɗanda abin ya shafa da kuma yaƙi da masu safarar haramtattun ƙwayoyi.
Gwamnan ya yabawa Hukumar NDLEA bisa ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga kowa da kowa da ya haɗa hannu domin kare makomar matasa da gina al’umma mai lafiya da zaman lafiya.
A nasa jawabin, Kwamandan NDLEA na Jihar Sokoto, Mustapha Gidado, ya bayyana shan miyagun ƙwayoyi a matsayin babbar barazana ga tsaro da lafiyar al’umma.
Shi ma Kodinetan Cibiyar Wayar da Kai Kan Hana Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu, Alhaji Abdulrazak Shehu, ya ce matsalar na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawaitar laifukan tashin hankali a cikin al’umma.
Hakazalika, Shugaban Ƙungiyar Masana Magunguna ta Najeriya reshen Jihar Sokoto, Dakta Aminu Ahmad Nyako, ya gargadi cewa miyagun ƙwayoyi na lalata jikin ɗan Adam tare da rusa makomar masu amfani da su.
“Ƙwayoyi na kashe mafarkin rayuwa,” in ji shi.
Taron ya samu halartar ɗalibai daga cibiyoyin ilimi daban-daban, shugabannin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.