Gwamnatin Amurka na Ci Gaba da Nemawa Kiristoci Kariya A Nijeriya

0 208

Amurka ta jaddada buƙatar ganin gwamnatin Najeriya ta bai wa Kiristocin ƙasar cikakkiyar kariya sakamakon hare-haren da Kiristocin ke fuskanta.

Allison Hooker babban jami’in ma’aikartar harkokin wajen Amurka, ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar da ya ke jagoranta ke ganawa da mahukuntan Najeirya a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ci gaba da cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta sani cewa Kiristoci na da damar gudanar da ibadunsu cikin ƴanci ba tare da wata tsangwama ba.

To sai dai tun daga farko har zuwa ƙarshen jawabinsa, jami’in wanda ke wakiltar ƙaƙƙarfar tawagar da shugaba Donald Trump ya tura, sam bai ambaci bai wa musulmi kariya ba, duk da cewa su ma waɗannan hare-hare na shafarsu.

Tawagar ta Amurka dai na ziyara a Najeriya ne, kwanaki biyu bayan da aka ruwaito cewa ƴanbindiga sun yi awon-gaba da mutane sama da 160 a wani ƙauye mai suna Kurmin Wali a jihar Kaduna, kuma har yanzu suna ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da su.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya fara bijiro da wannan batu na takura wa mabiya addinin Kirista a Najeriya, inda ya bayyana lamarin a matsayin ‘’kisan kiyashi’’.

To sai dai tun a lokacin mahukuntan Najeriya sun bayyana zargin na Trump a matsayin wuce gona da iri, tare da jaddada cewa a kullum suna iya ƙoƙarinsu domin kare illahirin al’ummar ƙasar ba tare da nuna wariya ko bambancin addini ba.

Leave a Reply