Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Aiwatar da Yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya Ta Kulla Ta 2025 A SLUK
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2025 tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) da Gwamnatin Tarayya ga malaman Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa (SLUK).
Amincewar za ta fara aiki ne daga watan Oktoba na shekarar 2026, tare da biyan basussukan watanni tara, daga Janairu zuwa Satumba na wannan shekara.
Sakataren ASUU na reshen SLUK, Salisu Yunusa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan ganawar da ƙungiyar ta yi da tawagar gwamnatin Jihar Jigawa ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026.
A cewarsa, shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar ne ya jagoranci tawagar, inda ya sanar da ƙungiyar amincewar da gwamnati ta bayar.
Ƙungiyar ASUU ta nuna godiyarta ga gwamnatin jihar da kuma shugabancin jami’ar bisa amincewa da aiwatar da yarjejeniyar.
Haka kuma, ta gode wa mambobinta bisa haƙuri, fahimta da kuma ci gaba da goyon bayan da suka bayar a tsawon fafutukar ganin an aiwatar da yarjejeniyar.
Ana sa ran matakin zai rage wa malaman jami’ar mallakar jihar nauyin da suke fuskanta, musamman ganin amincewar ta ƙunshi biyan basussukan watanni tara na farkon shekarar 2026.