Tinubu Ya Amince da Ware Naira Biliyan 45 Domin Sa Ido Kan Cututtuka A Filayen Jiragen Sama Biyar

0 5

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da ware naira biliyan 45 domin girka tsarin tsaron halittu da sa ido kan cututtuka a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa guda biyar, domin ƙarfafa ƙarfin Najeriya na gano sabbin barazanar cututtuka masu yaɗuwa da kuma ɗaukar matakan dakile su.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan ranar Laraba bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Ya lissafa filayen jiragen saman da za su amfana da shirin da suka haɗa da na Legas, Abuja, Kano, Fatakwal da Enugu.

A cewar ministan, za a aiwatar da aikin ne ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na tsawon shekaru 20, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar BioHealth Consortium.

Ya ce tsarin zai yi amfani da fasahohi da suka haɗa da binciken ruwan shara daga jiragen sama, ɗaukar samfuran iska da na saman abubuwa, da kuma na’urori na musamman domin gano ƙwayoyin cututtuka.

Pate ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen sa ido kan nau’o’in ƙwayoyin cututtuka masu haɗari, inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma ƙarfafa tsaron lafiya a iyakokin Najeriya.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner