Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da kwamitin yarjejeniyar kasuwanci babu shamaki

0 343

Kwamitin mai wakilai takwas yana karkashin jagorancin kwamishinan ciniki da masana-antu Alhaji Aminu Ahmed AK yayinda Darakta Janar ta invest Jigawa zata kasance sakatariyar kwamitin

Sauran wakilan kwamitin sun hadar da kwamishinonin kasafin kudi da na yada labarai da na lafiya da Darakta Janar na hukumar bunkasa tattalin arziki da kuma shugaban maaikata a fadar gwamnati

A jawabinsa bayan kaddamar da kwamitin, a babban dakin taro na gidan gwamnati, Gwamna Mallam Umar Namadi ya bukaci wakilan kwamitin da su yi aiki tukuru domin cimma manufar da aka sanya a gaba A jawabinsa na godiya shugaban kwamitin, Alhaji Aminu Ahmed AK ya godewa gwamnatin jiha bisa basu wannan dama tare da alkawarin yin aiki tukuru domin sauke nauyin da aka dora musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: