Adadin kudin da kasashen duniya ke kashewa wajen samar da tsaro ya karu da kashi 9 cikin 100

0 185

Wani rahoto ya bayyana cewa adadin Kudin da kasashen duniya ke kashewa wajen samar da tsaro ya karu da kashi 9 cikin 100, inda ya kai dala tiriliyan 2.2 a bara kamar yadda wata cibiyar bincike kan ayyukan soji ta Birtaniya ta bayyana.

Ana sa ran adadin kudin ya kara karuwa a wannan shekara ta 2024 saboda yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma rikicin da ake fama da shi a Ukraine, baya ga zaman tankiyar da ke zafafa a yankin tekun India da Pacific.

Kazalika sabon rahoton da Cibiyar Nazirin Ayyukan Soji ta Kasa da Kasa mai cibiya a birnin London  ta wallafa ya kuma ambaci barazanar da ke tsananta a yankin tekun Arctic da kuma yadda Koriya ta Arewa ke gina makaman nukiliya.

Har ila yau rahoton ya nuna damuwa kan China da kuma yadda sojoji ke juyin mulki a kasashen yankin Sahel, abubuwan da suka ce suna bada gudunmawa wajen haddasa rashin tsaro a duniya.

Rahoton ya ce, matakin Iran na bai wa mayakan Houthi makamai a Yemen da kuma jirage marasa matuka ga Rasha ya nuna yadda Tehran ke samun karfin fada-a-ji a yankin mai fama da rikici. Wani bangare na sakamakon da rahoton ya tattaro, ya nuna cewa, Rasha ta yi asarar manyan tankokin yaki 3,000 a lokacin fafata yakinta da Ukraine kuma tuni kasashen duniya suka dauki darasi daga yakin na Ukraine, abin da ya sa suke tanadin makamai a yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: