Shirin bayar da lamunin karatu na dalibai zai iya farawa nan da makonni biyu zuwa uku

0 258

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya ce shirin bayar da lamunin karatu na dalibai da ake jira zai iya farawa nan da makonni biyu zuwa uku.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a lokacin da wata tawaga daga kungiyar daliban Najeriya karkashin jagorancin shugabanta Lucky Emonefe ta kai masa ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ya kuma shaida wa daliban Najeriya da su tallafa wa shirin, inda ya ce an yi shi ne don tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga daukacin daliban kasar nan. Menema labarai, sun bayyana cewa tun a watan Yunin shekarar da ta gabata, shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan shirin ba da lamunin karatu na dalibai,  wanda aka yi jan kafa wajen aiwatar da shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: