An amince da bayar da Ton 42,000 na hatsi don rabawa ga marasa galihu

0 289

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya ce metric ton 42,000 na hatsi, da aka amince a fitar kwanan nan don rabawa ga marasa galihu na kasar nan za a bayar da shi kyauta.

Kyari ya bayyana haka ne a taron tattaunawa da manema labarai wanda ma’aikatar yada labarai ta tarayya da wayar da kan jama’a ta kasa ta shirya a jiya Laraba.

Ministan ya ce an kuma samar da injuna da matakan da suka dace don kara tabbatar da cewa mabukata cikin al’umma ne kawai ne suka samun tallafin abincin.

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta fitar da metric ton 42,000 na kayan abinci iri-iri daga baitul malin kasa da kuma kungiyar a matsayin kawo sauki kan matsalar karancin abinci a kasar nan.

Ministan ya kuma ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fitar da wata sanarwar da zata haramta biyan haraji sau biyu kan safarar kayan abinci a fadin kasar nan. Rahotanni sun ce biyan harajin sau biyu ya taimaka wajen hauhawar farashin kayan abinci da gwamnati ke fama wajen magance matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: