Nan ba da jimawa ba kasar nan za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta – Ganduje

0 220

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Ganduje, ya ce nan ba da jimawa ba kasar nan za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta, bisa la’akari da cigaban da aka samu a baya-bayan nan.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Arewa ta Tsakiya a Abuja.

Tun da farko, Sanata Ameh Ebute, tsohon shugaban majalisar dattawa wanda ya jagoranci tawagar, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya ga Ganduje kan salon shugabancinsa.

Ya kuma ce ziyarar ta zo ne domin karfafa masa gwiwar ci gaba da yi wa jam’iyyar APC aiki a matsayin shugabanta na kasa. Ya ce sun fito ne daga yankunan Benue, Plateau, Kogi, Niger, Nasarawa, Babban Birnin Tarayya da Kwara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: