Akalla mutane 25 ne aka gano sun kamu da cutar shan inna a jihar Kebbi

0 334

Wani malamin kiwon lafiya na hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko ta jihar Kebbi yace akalla mutane 25 ne aka gano sun kamu da cutar shan inna a kananan hukumomi tara na jihar.

Yusuf Umar Sauwa, ya bayyana hakan ne a yayin taron karawa juna sani na kwana daya da aka gudanar a cibiyar bada agajin gaggawa ta cutar Polio da ke Birnin Kebbi a jiya Laraba.

Da yake gabatar da rahoton bullar cutar shan-inna da aka gano a cikin wani jawabi ga masu ruwa da tsaki da sauran hukumomin bada tallafi da ke aiki a jihar, Umar Sauwa yace an samu rahoton bullar cutar a kananan hukumomi tara na jihar.

A cewarsa, ana amfani da dabaru da hanyoyi don tunkarar wuraren da lamarin ya shafa, inda ya kara da cewa suna kokarin ganin yadda za su dakile yaduwar cutar da inganta garkuwar yara. Ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Birnin Kebbi, Argungu, Suru, Bagudo, Gwandu, Aliero, Fakai, da Danko Wasagu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: