Putin ya ce ya fi son yin aiki tare da Shugaba Joe Biden maimakon Donald Trump

0 219

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce ya fi son yin aiki tare da Joe Biden maimakon Donald Trump bayan zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba.

Mista Putin ya kuma ce shugaba Biden ya fi zama gogaggen dan siyasa, fiye da wanda ya gada.

Sai dai ya ce Rasha za ta yi aiki da duk wanda jama’ar Amurkan suka aminta da shi.

Shugaba Putin ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wani dan jarida, RshaPavel Zarubin Mr Putin ya kuma yi watsi da batun shekarun Biden da kuma lafiyar kwakwalwarsa, yana mai cewa lafiya lau ya ganshi a lokacin da suka hadu shekaru uku da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: