Kungiyar New Incentives ta gabatar da taron bibiyar shirin taimakawa mata masu shayarwa da jarirai a jihar Jigawa

0 591

Karo na Uku Kenan, da kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta New Incentives ke gabatar da tarukan bibiyar irin cigaban da shirin taimakawa mata masu shayarwa da jarirai a Jigawa.

A dangane da kokarin da kungiyar ke yi, wajen yabawa zaqaquran ma’aikatanta na fadin kananan hukumomi da jami’an hukumar lafiya matakin farko a Jigawa, New Incentives ta karrama wasu asibitoci da jami’ai da suka yi fice da kuma nuna kwazo a aikin zaqulo kananan yara da basu kulawa da kungiyar ke yi a Jigawa.

A taron, an gabatar da kyaututtuka daban-daban ga kananan hukumomi 5 dake kan gaba a yawan bayar da alluran rigakafi, da yawan rigistar jarirai, inda aka ayyana kananan hukumomin Sule Tankarkar, da Miga, da Hadejia, da Jahun da Babura da karamar hukumar Gwaram a matsayin wanda suka yi fice a Jigawa tare da basu kyautar Naira dubu 150 ga kowanne rukuni hade da lambar girmamawa ga kowacce tawaga.

Sa’annan kuma an bayar da lambar yabo ta musamman ga kananan hukumomi 3 da suka fi kwazo a jihar, kuma kowace karamar hukuma ta samu Naira dubu 300,000 ga asibitocin kula da kananan yara, domin amfani da shi wajen karfafa tsarin kiwon lafiya, kamar gyaran asibitoci, samar da kayan aiki, da kula da sashen sanyaya allurai na karamar hukumar.

Kazalika an, bayar da lambar yabo ga jami’an jiha a lokacin bikin, inda aka zaqulo masu ruwa da tsaki, aka karramasu sakamakon hidimar da suke yi na inganta aikin bayar da rigakafin yau da kullum, wanda suma aka basu Naira dubu 700,000 don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya.

Inda daga karshe aka bayar da lambar yabo ga manajan da yafi nuna kwazo a shirin NI-ABAE a jihar, wanda aka bashi kyautar N30,000 domin kara masa kaimi a aikin da yake.

A baya dai cikin watan Disambar 2018, tawagar New Incentives a Jigawa ta yi bikin karbar rajistar jarirai dubu 100,000 a duk jihohin uku a nan Jigawa.

Taron da ya gudana ne a Ringim, inda ya samu halartar babban sakataren kungiyar SPHCDA ta jihar Jigawa a wancan lokacin, Dakta Kabir da tawagarsa da kuma wakilin kwamishinan lafiya da wakilan mai martaba Sarkin Ringim da kuma shugaban karamar hukumar.

Rahoton sakamakon binciken da IDinsight ya fitar a cikin shekarar 2020 ya nuna cewa shirin ya yi tasirin gaske, inda ya fadada a cibiyoyin lafiya a matakin farko a wurare daban-daban. Yayin da aka samu cigaba a yaki da cutar kyanda da kasha 62 cikin 100.

An samu cigaba a bangaren cibiyoyin lafiya dake bayar da agaji da taimakon kananan yara da kasha 108 cikin 100.

A farkon 2021, shirin “All Babies are Equal” wato Da na kowa ne, ya fadada aiyukansa zuwa asibitoci 98. Ya zuwa karshen shekarar, ta fadada zuwa asibitoci 986 a fadin Zamfara, Katsina, da Jigawa.

A shekarar 2022, shirin ya sake fadada zuwa Bauchi, Gombe, da Sokoto, inda ya kai sama da asibitoci 2,000 a tsakiyar shekarar. A watan Oktobar, 2022, New Incentives ta sake bikin shigar jarirai da yawa a cikin 2022 fiye da duk shekarun da suka gabata  a hade.

Kuma a tsakiyar watan Disamba aka yi bikin shigar da jarirai miliyan 1 a cikin shirin.

A cikin shekarar 2023, shirin na All Babies ya ci gaba da fadada zuwa Kano, Kaduna, da Kebbi sannan ya shigar da jarirai miliyan 2 a watan Satumba.

Ya zuwa watan Janairu, shirin All Babies ya samu nasarar shigar da jarirai sama da 618,000 a Jigawa kadai, inda aka raba sama da naira biliyan 2 da miliyan 100 ga iyayen yaran, tare da kara yawan alluran rigakafin da ake baiwa jariran zuwa miliyan 8.7.

A duk fadin jihohin da ake gudanar da aiki, shirin na All Babies ya dauki jarirai sama da miliyan 2 da dubu 700, inda aka raba sama da naira biliyan 8. Da miliyan 400, tare da kara yawan Alluran rigakafin zuwa sama da guda miliyan 34.

Daraktan masu ruwa da tsaki da hulda da jama’a Nura Muhammad, ya ceMuna sa ran ci gaba da hadin gwiwar da gwamnatin jihar Jigawa da kananan hukumominta kan kokarin da muke wajen kara wayar da kan jama’a game da muhimmancin allurar rigakafin yau da kullum tare da karfafa wa masu shayarwa da su kawo ‘ya’yansa domin yin rigakafin”. In ji shi.

Bikin na ranar, ya samu halartar darurwan jami’an lafiya matakin Farko a jihar Jigawa da wakilan kungiyoyin lafiya da tallafawa kananan yara na Majalissar Dinkin Duniya irinsu, WHO, UNICEF, MRITES da masu baiwa gwamnan Jigawa shawara kan harkokin lafiya da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: