Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin naira dubu 35 da ta fara biyan ma’aikata domin rage radadin illar cire tallafin man fetur ga ma’aikatan ƙasar.
Gwamnatin ta kuma roki kungiyar kwadagon da su janye yajin aikin da suka shirya yi na kwanaki 14.
Karamar ministar Kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bada wannan tabbacin a Abuja a wajen wani taro da shugabannin ƙungiyoyin kwadagon biyu da aka yi kan wa’adin da suka bai wa gwamnati na tafiya yajin aiki idan ba ta cika musu bukatunsu ba a cikin makonni biyu.
An dai cimma yarjejeniyar ne ranar 2 ga Oktoba, 2023 mai dauke da abubuwa 16 da suka hada da ƙarancin albashin ma’aikata da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata duk wata da dai sauransu.
Onyejeocha ta kuma ce gwamnati ta kara kaimi wajen ganin an kammala aiwatar da wannan yarjejeniya. Ministar ta kira taron ne domin bayyana wa ƙungiyoyin kwadagon yadda ake aiwatar da yarjejeniyar, da kuma jaddada aniyar gwamnati kan yarjejeniyar.