Sama da ma’aikatan jinya dubu 42 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru uku da suka gabata

0 173

Farfesa Faruk Abubakar, Rijistaran kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa, ya ce sama da ma’aikatan jinya dubu 42 ne suka bar kasar a cikin shekaru uku da suka gabata.

Abubakar ya nuna damuwarsa kan wannan lamari, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da ma’aikatan jinya ke takawa a fannin kiwon lafiya.

Da ya ke zantawa da gidan Talabijin na Channels TV a jiya Talata, Abubakar ya ce, cikin shekaru uku da suka gabata, sama da ma’aikatan jinya dubu 42 ne suka bar kasar nan kuma kasar na bukatar su. A cewar sa Manufofin gwamnati musamman ajandar Renew Hope na yanzu, tsare-tsare da yawa suna tafe, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta fito da tsare-tsare masu yawa inda za a inganta tsarin kiwon lafiyar Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: