Gwamnatin Jigawa ta tunatar da Alkalai muhimmancin rantsuwar da suka dauka yayin gudanar da ayyukansu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta tunatar da Alkalai muhimmancin rantsuwar da suka dauka yayin gudanar da ayyukansu.
Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan a wajen bude taron bitar kwanaki biyu da hukumar kula da alamurran shari’a ta jihar ta shirya ga sabbin Alkalai da aka nada.
Gwamnan ya ce kuskure guda daga Alkalin kotu na iya jefa al’umma cikin rudani da rashin fahimtar juna.
Malam Umar Namadi ya kara da cewa alkalai na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.
Dan haka ya yaba wa hukumar kula da ayyukan shari’a ta jiha bisa kokarinta na shirya wannan bita domin ba sabbin Alkalai horan kwarewar aiki da za su taimaka musu wajen gudanar da aikinsu da tsoron Allah.
A nasa jawabin, babban mai sharia na jiha , Mai Shari’a Umar M. Sadiq, ta hannun alkalin alkalai na jiha Sani Salihu, ya ce wannan bita zata zama dandalin musayar ilimi da bunkasa kwarewa.
Ya bukaci sabbin Alkalai da su kasance masu yanke hukunci da gaskiya kuma su nisanci aikata miyagun dabi’u da karbar rashawa da kuma zuwa aiki da wuri. Shima ya yaba da goyon bayan da bangaren shari’a ke samu daga gwamnati domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata a jihar.