Gwamnatin Jigawa ta yi rijistar manoma 100,000 cikin tsarin noma na zamani

0 139

Gwamnatin Jigawa ta yi rijistar manoma 100,000 cikin tsarin noma na zamani da amfani da fasahar zamani a kokarinta na sauya fasalin bangaren noma a jihar.

Kwamishinan yada labarai, matasa da wasanni na jihar, Sagir Musa, ya bayyana hakan ne a Dutse yayin da yake gabatar da nasarorin gwamnatin Umar Namadi cikin Shekaru biyu.

Ya ce an cimma kashi 75 cikin 100 na shirin, inda aka raba taki, da iri da kayan noma ga manoma 85,000 da kuma horar da 4,200 daga cikin masu kiwon kaji 5,000 da aka sa a gaba. Haka kuma, an samu ci gaba a kiwon shanu da ya hada da tsarin inganta jinsinsu, da samar da rijiyoyin noman rani har na hekta 3,800 a yankin kogin Hadejia.

Leave a Reply