Gwamnatin jihar Jigawa ta nanata kudirinta na samar da isassun gidaje domin raya biranen jiharnan.

Kwamishinan kasa da gidaje da raya birane, Sagir Musa Ahmed ya bada wannan tabbaci a lokacin daya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani a Gumel.

Ya bayyana kudirin gwamnatin jiha na gina rukunin gidaje dari biyar a kowacce masarauta.

Kwamishinan ya kuma shaidawa mai martaba sarki kudire kudiren gwamnati na fara yiwa gidaje rijista da za a fara nan bada jimawa ba.

A nasa jawabin, mukaddashin babban sakataren ma’aikatar kuma Babban Mai Safiyo na jiha Mallam Abdullahi Hassan yace yiwa gidaje rijista yana da muhimmanci domin kuwa zai taimakawa gwamnati wajen yin tsare tsare. Da yake mayar da jawabi, mai martaba sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani, ya yabawa gwamnatin jiha bisa kyawawan manufofinta na na ciyar da jiharnan gaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: