Gwamnatin Jigawa za ta tantance yan fasho dake karkashin tsarin adashen gata a jihar

0 667

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da shirin gudanar da tantance yan fasho dake karkashin tsarin adashen gata na fansho.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Muhammad Dagaceri, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a jiya a ofishin fansho da ke Dutse.

Taron ya haɗa da shugabannin Ƙungiyar Tsofaffin Ma’aikata ta kasa, reshen Jihar Jigawa, domin shirya yadda za a gudanar da tantancewar da za ta fara ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.

A cewar Dagaceri, wannan tantancewa za ta taimaka wajen sabunta tsarin biyan hakkokin yan fansho, gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka faru a cikin shekaru ukun da suka gabata, da kuma tabbatar da daidaito a tsarin biyan fansho.

Ya jaddada cewa ba a yi wannan tantancewa domin cin zarafin kowa ba, sai dai domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gwamnati.

Shi ma Babban Akanta na Jihar, Abdullahi Shehu, ya bayyana a taron cewa wannan tantancewa za ta ba wa masu ritaya damar sabunta bayanansu da kuma cike duk wasu bayanai da suka bace a takardun biyan su.

Leave a Reply