Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta cigaba da baiwa hukumar Hisba kulawa ta musamman domin gudanar da aikin ta yadda ya kamata

0 85

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta cigaba da baiwa hukumar Hisba kulawa ta musamman domin gudanar da aikin ta yadda ya kamata.

Mataimakin gwamnan jiha Mallam Umar Namadi ne ya bada wannan tabbacin a gurin taron tattaunawa da hukumar ta shirya a dakin taro na cibiyar horas da ma’aikata dake Dutse.

Mataimakin gwamnan wanda ya yi dogon bayani akan ayyukan alkahairi da hukumar Hisbah take yi, ya ce gwamnati zata samar da kyakkyawan yanayi da zai kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da aikin su.

Malam Umar Namadi ya kara da cewar samar da harkar ilimi da lafiya da tsaro da samarwa matasa aikin yi da harkar noma na cikin kudurorin sa idan ya samu nasarar hawa kan kujerar gwamnan jihar.

A nasa jawabin, babban kwamandan Hisba na jihar Jigawa Malam Ibrahim Dahiru Garki ya ce an shirya wannan taron ne domin tattauna al’amuran da zai kawo cigaban jiha da kuma nuna goyon baya su ga dan takarar gwamnan jiha Malam Umar Namadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: