Darajar kuɗin naira za ta sake faɗuwa wanwar yayin da shekarar 2022 ke ƙarewa a Najeriya

0 181

Masana harkokin sauyin kuɗi a Najeriya na ganin darajar kuɗin naira za ta sake faɗuwa wanwar yayin da shekarar 2022 ke ƙarewa, musamman a farashin gwamnati.

Ana canzar da dala ɗaya kan naira 457 a farashin gwamnati a jiya Alhamis, fiye da naira 450 da aka canzar da ita a makon da ya gabata.

A kasuwar bayan fage kuwa ana canzar da dalar kan naira 740.

Sauya wasu takardun naira a watan nan da kuma rage adadin kuɗin da ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni za su iya cirewa a kullum na ci gaba da ɗumama harkokin kuɗi a kasar nan.

Bayan matsin lamba babban bankin kasa CBN ya amince ya kara adadin daga naira dubu 500 zuwa naira miliyan 5 a kowane mako ga kamfanoni, naira dubu 100 daga naira dubu 20 ga daidaikun mutane a kowace rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: