Gwamnatin tarayya tace ta kashe sama da naira biliyan 5 wajen gyaran chaji ofisoshin yan sanda

0 78

Gwamnatin tarayya a jiya alhamis tace ta kashe sama da naira biliyan 5 wajen gyaran chaji ofisoshin yan sanda a duka sassan kasar nan a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.

Haka kuma ta bayyana cewa ta samar da kayan aiki na zamani ga hakumar yansandan da makarantun hoswa da cibiyoyin kiwon lafiya na yansanda a fadin kasa.

Ministan lura da ayyukan yansanda na kasa Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka yayin da yake jero nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cimma daga shekarar 2015 zuwa tanade-tanade masu Gajere da dogon zango har zuwa 2023, a wata ganawa da manema labarai wanda ma’aikatar watsa labarai da al’adu ta shirya.

Dingyadi ya zayyano wasu barikin yansanda da yace gwamnatin tarayya ta gyara da suka hada na jihohin Kebbi, Edo, Borno, Yobe, Gombe, Bauchi, Plateau, Abia, Bayelsa, Nasarawa, Niger, Sokoto, Ogun, Lagos da kuma birnin tarayya Abuja.

Ya sanar da yan jarida cewa gwamnatin ta samar da kayan aiki na sama da naira triliyan 1 Da biliyan 300 a ofisoshin hakumar dake birnin tarayya Abuja, sannan ta samar da kayan aiki na zamani.

A wani batun kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa ta sabunta kokarinta na kyautata rayuwa da walwalar yansanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: