Jam’iyyar APC tana zargi PDP da shirya ta da hargitsi don hana zaben 2023

0 89

Kwamitin yaƙin neman zaben ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya zargi babbar jam’iyyar adawa ta PDP da shirin ta da hargisti don hana gudanar da zaben ƙasar na 2023.

Daraktan yada labaran kwamitin yakin nema zaben Bola Ahmad Tinubu a APC, Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da suka wallafa a shafin kwamitin na Twitter, yana mai kira ga hukumomin tsaro a Najeriya da su gaggauta gayyatar shugabanin jam’iyyar PDP don amsa tambayoyi.

“Mun lura cikin damuwa cewar irin kalaman da ke ƙunshe da sanarwar da PDPn ta fitar , na nuni ƙarara da lama ce ta zasu kawo hargitsin a loakacin zaɓe mai zuwa, kuma mun sami bayanai masu ƙarfi kan wadan ke tayar da hargiutsin a wasu sassan ƙasar, ”a cewar sanarwar.

Ya ce kiran ya zama wajibi biyo bayan wata sanarwa da PDP suka fitar kan “sahihin zabe” da ke cewar sun zargin wasu daidaiku na kokarin kawo hargitsi a zaben 2023.

Keyamo ya nanata cewar lallai ne PDP sai ta samar da bayanai dangane da “wajen da aka yi taron da wadan da suka halarci taron; da sunaye wadan da ke taayr da hargitsin ta hanyar kai hare hare oishin hukumar zaben kasar INEC. Wannan bayanai dole ne su hada da bayanann wadan ke daukar nauyin su, idan akwai

Keyamo ya ce sanarwar da PDP ta fita na zuwa ne sao’i 48 da wata kotu ta yankewa ɗaya daga cikin shugabnin PDPn hukunci, kan laifukan da ke da alaka da zabe, lokacin da ta ke mulki, manuniya ce da ke nuna yadda maratabar PDPN ke zubewa kamar yadda BBCHausa ta wallafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: