Gwamnatin jihar Jigawa ta saki kudi sama da naira biliyan 1 da miliyan 200 ga rukunin ma’aikatan fansho

0 131

Gwamnatin jihar Jigawa a jiya ta ce ta saki kudi sama da naira biliyan 1 da miliyan 200 ga rukunin ma’aikata daban-daban wadanda ke cikin shirin fansho daga watan Yuli zuwa Augusta.

Babban Sakataren Hukumar Fansho na Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi, Hashim Ahmad Fagam ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Dutse.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya ruwaito cewa daga cikin naira biliyan 1 da miliyan 200, an biya naira miliyan 872 da dubu 700 a matsayin kudin fansho yayin da aka biya naira miliyan 295 da dubu 700 a matsayin hakkokin mamata.

Hakanan, an biya naira miliyan 51 da dubu 300 a matsayin ragowar fanshon mamata, yayin da aka biya naira miliyan 2 da dubu 700 a matsayin ragowar kashi takwas cikin na adashen gata.

Da yake sanar da kididdigar kudaden watan Yuli, babban sakataren ya ce an saki jimillar naira miliyan 420 da dubu 690 ga wadanda suka yi ritaya su 192 daga jihar a matsayin hakkokin ritaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: