Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yi taro da manyan masu ruwa da tsaki game da tsaro

0 125

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yi taro da manyan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Taron wani bangare ne na kokarin inganta zaman lafiya bayan hare-haren baya-bayan nan a karamar hukumar.

Da yake jawabi a taron da aka gudanar a gidan Gwamnati da ke Jos, Simon Lalong ya gode wa masu ruwa da tsaki kan taimakon da suka bayar wajen dakile tashin hankali a tsakanin al’ummominsu da kuma taimakawa hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Ya yi musu bayanin matakan da gwamnati ke dauka don kawo karshen kalubalen tsaro a jihar sannan ya yi nuni da cewa cigaba da tattaunawa da yin aiki zai taimaka wajen zaman lafiya a jihar.

Da yake jawabi a karshen ganawar ta sirri, Mataimakin Babban Limamin Jos, Ghazali Adam, ya ce masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yanke shawarar zama tare da juna da daidaita sabanin da ke tsakaninsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: