GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA SHIGAR DA TSARIN ALMAJIRAI CIKIN KARATUN ZAMANI TA HANYAR GYARA MAKARANTUN TSANGAYA
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi tare da gabatar da shirin gyare-gyare masu fadi don magance matsalar karancin ilimi da kuma karfafa makarantu a fadin jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa binciken da aka gudanar ya nuna yara takwas cikin goma a aji daya na firamare ba sa iya karatu ko rubutu, lamarin da ya ce ya zama dole a dauki matakan gaggawa.
Daga cikin matakan, gwamnati ta raba ma’aikatar ilimi zuwa bangaren Ilimin Firamare da na Sama domin rage cunkoso da kuma tabbatar da gudanar da aiki cikin tsari, tare da daukar sama da sabbin malamai dubu goma a cikin watanni kadan don magance karancin malaman makarantu.
Haka kuma an kafa kwamitocin kula da makarantu da kuma kungiyoyin iyaye mata domin sa ido kan halartar malamai da tabbatar da yara na zuwa aji, tare da hada kai da wani kamfani na Ingila mai suna NewGlobe domin inganta karatu da lissafi.
Gwamnatin ta kuma shigar da tsarin Almajirai cikin karatun zamani ta hanyar gyara makarantun Tsangaya da gina manyan makarantu masu zaman kansu, tare da saka hannun jari mai yawa a cibiyoyin koyon sana’o’i da horas da malamai, abin da Gwamna Namadi ya ce shi ne tubalin makomar ilimi a Jihar Jigawa.