Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kisan Jami’an Soji 2 da wasu fararen hula 32 a karamar hukumar Kauru ta Jihar

0 93

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kisan Jami’an Soji 2 da wasu fararen hula 32 biyo bayan hare-haren da aka kaddamar a karamar hukumar Kauru ta Jihar.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya, inda ya ce mutane da dama ne suka samu raunika, baya ga gidajen da aka kone a yankin.

A wani labarin kuma, Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International, ta yi Allah wadai da kisan mutane tare da lalata wuraren Ibada a yankin Kagoro na karamar hukumar Kauru ta Jihar.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta Amnesty International, ta koka kan yadda yan bindigar suka aiwatar kisan tare da shafe sama da awa 2 suna cin karen su ba babbaka, duk da irin gudunmawar da Jami’an tsaro suka bayar.

Haka kuma yan bindigar sun yi nasarar farmakar gururuwa 3 tare da raba daruruwan mutane da muhallan su.

Amnesty International ta bukaci gwamnatin tarayya ta kare rayukan yan kasar ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: