An kaddamar da kwamati domin fara duba tsarin koyarwar makarantun Dutse Mega school da kuma Santami International School dake Garki a jihar Jigawa

0 45

Kwamishinan ilimi kimiyya da fasaha na jihar Jigawa, Dakta Lawan Yunusa Danzomo, ya kaddamar da kwamati mai wakilai 14 domin fara duba tsarin koyarwar makarantun Dutse Mega school da kuma Santami International School dake Garki.

Da yake kaddamar da kwamatin, kwamishinan ya ce gwamnati ta samar da makarantun ne domin inganta kwazon dalibai da hakan zai basu damar gogayya da sauran takwarorin su na fadin kasar nan.

An daurawa kwamatin alhakin samar da yadda harkokin karatu zasu gudana a makarantun da tsarin da daliban makarantar zasu kasance da kuma tsarin bada damar shiga makarantun.

Kwamatin na karkashin jagorancin babbar Sakatariyar Maa’aikatar, Hajiya Safiya Muhammad da sakataren zartarwa hukumar ilimin manya, Dakta Abbas A Abbas a matsayin mataimaki, yayin da Kamilu Ibrahim zai kasance sakataren kwamatin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: