- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan dubu 92 da miliyan 100 domin gina sararin sauka da tashin jiragen sama na biyu a filin jiragen sama na kasa da kasa na Nmandin Azikiwe dake Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa amincewar majalisar yazo ne kasa da awanni 24 bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon gini a filin jiragen saman kasa da kasa na Murtala Muhammad dake Lagos.
A wajen kaddamar da ginin, shugaban kasar ya umarci minister kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa da ta samar da kudade na musamman domin gina sararin sauka da tashin jiragen sama na biyu a filin jiragen saman na Abuja.
Da yake yiwa manema labaran fadar shugaban kasa jawabi dangane da zaman majalisar, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta yau a Abuja, ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, yace gwamnati za tabi hanyar da tafi wajen samun kudaden aiwatar da sauran ayyuka.
A cewarsa, ana sa ran kammala aikin ginin sararin sauka da tashin jiragen saman cikin watanni 12 masu zuwa.