Akalla mayakan Boko Haram da na ISWAP dubu 7 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya a makon da ya gabata.

Kwamandan Operation Hadin Kai, Christopher Musa, shine ya sanar da haka a yau yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Maiduguri.

Christopher Musa yace fatattakar da sojoji ke yiwa mayakan ISWAP da na Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas na cigaba da haifar da da mai ido.

Christopher Musa yayi bayanin cewa ana sa ran sojojin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki zasu tantance mayakan da suka mika kai tare da iyalansu kafin a sauya musu rayuwa.

Kwamandan yace sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro za su cigaba da lalubo hanyoyi kawo karshen ta’addancin Boko Haram cikin gaggawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: