Dillalan man fetur na Arewacin Najeriya suna barazanar tsindima yajin aiki biyo bayan kin biyan su kudin safarar man fetur

0 131

Dillalan Man fetur karkashin Kungiyar Dillalan Man fetur na Arewacin Najeriya sun yi barazanar tsindima yajin aiki biyo bayan kin biyan su kudin safarar fetur din tun cikin watan Yunin 2021.

Da yake jawabi a madadin kungiyar a Kano Alhaji Gana Girgiri ya ce rashin biyan kudaden safarar man fetur din ya sanya wasu daga cikin yan kasuwar su hakura da kasuwancin, inda ya kara da cewa mambobin kungiyar zasu janye ayyukan su gaba daya matukar gwamnati bata dauki matakan biyan su hakkokin su ba.

Haka kuma ya ce duk da irin kokarin da kungiyar ta yi domin ganin cewa an biya su hakkokin su na sifirin Fetur din, babu wani cigaba daga wuri gwamnati na daukar matakan.

Wani mamba a kungiyar Alhaji Jamilu Maitama, ya fadawa manema labarai cewa mambobin su da yawa a yanzu haka sun hakura da kasuwancin biyo bayan kin biyan hakkokin su da gwamnati tayi na Biliyoyin Nairori.

A cewarsa, tabbas karancin man fetur da ake fama da shi zai cigaba matukar gwamnati ta bari suka janye ayyukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: