Shugaban kasa Buhari da gwamnonin jam’iyyar APC sun kasa tsayar da magana akan shugabancin jam;iyyar APC

0 24

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ganawar sirri da daukacin ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC a babban taronta na kasa da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan daukar hoto, Sunday Aghaeze, ya tabbatar da hakan da yammacin jiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa, ‘yan takarar sun samu jagorancin shugaban riko na kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Kamfanin Dillancin Labaran ya bayar da rahoton cewa, wadanda abin ya shafa sun hada da George Akume, Tanko Al-makura, Sani Musa, Abdullahi Adamu, Mohammed Saidu-Estu, Abdulaziz Yari da Ali Modu Sheriff.

An rawaito cewa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari suma sun halarci zaman ganawar shugaban kasar tare da ‘yan takarar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: