Da gaske ne zan tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar mu ta PDP – Atiku

0 18

tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana a hukumance cewa zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani gagarumin taron da aka gudanar a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja.

Taron ya samu halartar manyan baki da dama ciki har da gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri.

Tsohon mataimakin shugaban kasar a yayin da yake lissafo wasu tsare-tsare da yake yi wa kasarnna, ya sha alwashin mika mulki ga matashi idan aka zabe shi.

Ya kuma ce yana da niyyar mayar da hankali ne kan muhimman abubuwa guda biyar da suka kunshi hadin kan Najeriya, tsaro, tattalin arziki, ilimi da kuma karin madafun iko ga sassan tarayya.

Atiku Abubakar ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da gazawa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya wanda a cewarsa shi ne babban abin da ya sa a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: