Ma’aikatar ilmi, kimiyya da fasaha ta jihar Jigawa ta fara rangadin duba makarantun gaba da sikandire

0 85

Ma’aikatar ilmi, kimiyya da fasaha ta jihar Jigawa ta fara rangadin duba makarantu a wani mataki na tabbatar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a makarantu.

A sanarwar da maaikatar ta fitar ta hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Wasilu Umar Ringim, tace a lokacin ziyarar an tura kwamishina da babbar sakatariya da sauran shugabannin sassan hukumomin ma’aikatar zuwa makarantu domin duba harkokin koyo da koyarwa a makarantun.

Sanarwar tace a lokacin ziyarar, masu duba makarantu zasu lura da harkokin koyo da koyarwa da duba tsarin jaddawalin koyarwa na malaman makarantun.

Sanarwar ta rawaito kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jiha, Dr Lawan Yunusa Danzomo, yana kira ga malaman da suke cikin masu ziyarar da su sanya kaimi tare da yin gaskiya da adalci kan abubuwan da zasu gani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: