Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an sake gano wasu gawarwaki uku a kananan hukumomin Jema’a da Kaura, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon rikicin na baya bayan nan zuwa 37.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

A wani labarin kuma, an kaso wasu mutane 75 da aka yi garkuwa da su a kauyen ‘Yar Katsina da ke gundumar Kekun Waje a karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

An yi garkuwa da mutanen da aka sako a wasu manyan hare-hare guda biyu da aka kai kauyen cikin watanni biyun da suka gabata.

A baya dai ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutanen kauyen su 61, sannan bayan kwanaki 36, suka kai farmaki cikin kauyen tare da yin awon gaba da wasu mutane 15.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: