Jadawalin dokokin babban zaben 2023 zai kammala watanni 10 kafin zaben – Hukumar Inec

0 99

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce jadawalin dokokin babban zaben 2023 zai kammala watanni 10 kafin zaben.

Za’a fara gudanar da zaben ne a watan Fabreru na 2023, wanda hakan ya ke nuni da cewa kafin karshen watan Afrilu hukumar ta INEC zata fitar da Jadawalin zaben da ke tafe.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwar da hukumar INEC ta fitar cikin wani sakon mujallar hukumar a jiya.

Sanarwar ta ce Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi Jagororin Gidauniyar MacArthur a ofishin sa da ke Abuja.

Shugaban hukumar ya tunasar da cewa a shekarar 2019, hukumar ta fuskanci kalubalan lokaci, biyo bayan rashin tabbaci wanda ya dabaibaye jadawalin da hukumar ta tsara.

Haka kuma ya ce INEC ta sanya hannu kan ka’idojin zaben na shekarar 2019 a ranar 19 ga watan Janeru makonni kalilan kafin babban zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: