Ya kamata a tsagaita wuta tunda mun yarda da fasa shiga kungiyar NATO – Shugaban kasar Ukraine

0 85

Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelenskyy a daren jiya yace a shirye yake ya tattauna tare da tabbatar da janyewa kasarsa wajen neman shiga kungiyar NATO domin a tsagaita wuta.

Ya kara da cewa a shirye yake ya tattauna akan yankin Crimea da gabashin yankin Donbas da ‘yan awaren da Rasha ke goyawa baya suke rike da iko bayan an tsagaita wutar tare da daukar matakan samar da tsaro.

Shugaba Zelenskyy tun a jiya da safe yace ganawa da shugaba Vladimir Putin na Rasha na da amfani wajen fuskantar matsayarsu.

A ranar 24 ga watan Fabrairu Rasha ta kaddamar da hari kan Ukraine.

Kamar yadda ofishin hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya ya sanar, yakin wanda ya kusa shafe wata guda, yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula 925 tare da jikkata wasu dubu 1 da 400.

Leave a Reply

%d bloggers like this: