Labarai

Hukumar kiyaye hadura ta kasa tace an samu haduran mota sau 1028 da mutuwar mutum 128 a jihoshin Jigawa, Kano, Kaduna da Katsina a cikin wata 3

Hukumar kiyaye hadura ta kasa tace an samu haduran mota sau dubu 1 da 128 da mutane 121 suka mutu a jihoshin Jigawa, Kano Kaduna da Katsina, tsakanin watan Janairun bana zuwa Maris da muke ciki.

Kwamandan hukumar na shiyyar Zaria, Abubakar Tata Murabus, ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai jiya a Zarian jihar Kaduna.

Ya kara da cewa matafiya 536 sun samu raunuka daban-daban cikin watannin.

A cewarsa, mafiya yawan haduran sun auku akan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano.

Ya danganta yawaitar aukuwar haduran mota da mace-mace akan yawan gudun da ya wuce hankali da lodin da ya wuce kima da kuma tafiye-tafiyen cikin dare.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: