

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta zartar da kudirin dokar hana bahaya a sarari yayin zamanta na yau.
A karkashin dokar, duk wanda aka kama ya aikata laifin bahaya a sarari, za a yanke masa hukuncin daurin watanni 10 a gidan gyaran hali, ko zabin biyan tarar kudi akalla naira dubu 5 ko hidinmtawa al’umma.