Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta sanar da kama mutane 99 a kananan hukumomin Kazaure da Dutse bisa laifin aikata badala.

Kwamandan Hisbah na jiha, Mallam Ibrahim Dahiru, wanda ya zanta da manema labarai yau a Dutse, yace wadanda aka kama da suka kunshi mata 54 da maza 44, an kama su ne a ranakun 16 da 17 ga watan Maris a wasu sumame daban-daban da jami’an hukumar suka kaddamar.

Yayi bayanin cewa mutane 91 cikin wadanda aka kama, da suka hada da mata 49 da maza 42, an kama su a ranar 16 ga watan Maris, bayan wani sumame da aka kai Gada Kazaure.

A cewarsa, wadanda aka kama, ana zarginsu da aikata badala tsakanin mata da maza.

Kwamandan yayi bayanin cewa ragowar mutane 8 da aka kama da suka hada da mata 5 da maza uku, an kama su a ranar 17 ga watan Maris a Dutse.

Ya kara da cewa an kwace kwalabe 8 na giya a lokacin sumamen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: