Fadar shugaban kasa tace jam’iyyar PDP mai adawa za ta mutu muddin fatan da take yiwa Najeriya shine a gudanar da zanga-zanga

0 92

Fadar shugaban kasa tace jam’iyyar PDP mai adawa za ta mutu kamar yadda daya daga cikin ‘yan takararta na shugaban kasa yayi hasashe, muddin fatan da take yiwa kasarnan shine gudanar da zanga-zanga akan halin da ake ciki, wacce tafi ta EndSARS muni.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman akan kafafen yada labarai, Femi Adesina, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa jiya a Abuja.

Ya bukaci PDP da ta mayar da hankali wajen hada kan kasarnan akan take tunanin barkewar zanga-zangar da tafi EndSARS muni, wacce aka samu asarar rayuka da tashe-tashen hankula.

Yace jam’iyyar PDP ta badawa kanta kasa a fuska yadda ta nuna cewa burinta kawai shine wanzar da rikici a kasarnan domin samun damar komawa karagar mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: