Gwamnatin jihar Kebbi ta kaddamar kwamitin binciko abubuwan da suka faru na fasa rumbun gwamnati

0 180

Gwamnatin jihar Kebbi ta kaddamar da wani kwamiti mai mutane 13 da aka dorawa alhakin binciko abubuwan da suka faru na satar kayan abinci da kuma tsara dabarun yadda za’a hana faruwar hakan nan gaba.

Kwamitin wanda kwamishinan noma da albarkatun kasa Alhaji Shehu Mu’azu zai jagoranta, an baiwa kwamitin wa’adin kwanaki biyar domin gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kwashe kayan abinci ba bisa ka’ida ba daga rumbun ajiyar gwamnati da ke Birnin Kebbi. .

An yanke shawarar kafa kwamitin ne yayin wani taron majalisar zartarwa ta jihar wanda mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Abubakar-Tafida ya jagoranta a Benin Kebbi a ranar Litinin din da ta gabata. Majalisar ta kuma amince da bayar da tallafi na Naira biliyan 3.34 domin rage wa tallafawa maniyatan aikin hajjin bana su 3,344.

Leave a Reply

%d bloggers like this: