An sace wasu dalibai a jihar Delta da ba a tantance adadinsu ba

0 107

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta tabbatar da sace wasu dalibai da ba a tantance adadinsu ba.

Kakakin ‘yan sandan Edafe Bright ya wallafa a shafinsa X cewa, rundunar na sane da wannan a’lamari.

Rahotannin sun ce daliban na tafiya ne cikin wata ‘yar karamar motar bas a yankin karamar hukumar Ughelli a ranar Juma’a. Kakaki Bright ya ce ba a tuntubi kowa kan neman biyan kudin fansa ba amma suna iya bakin kokarinsu don ganin an ceto daliban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: