Gwamnatin jihar Yobe ta rufe wasu cibiyoyi da asibitoci masu zaman kansu guda bakwai a jihar

0 260

Dokta Yusuf Ngamdu, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Lafiya ta jihar shi ne ya bayyana hakan jiya a Damaturu.

Ngamdu ya ce wuraren da abin ya shafa suna gudanar da ayyukansu ne ba bisa ka’ida ba ta hanyar bayar da takardun shaida da kuma gudanar da ayyukan jinya fiye da yadda doka ta tanada.

Ya ce wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa sun hada da Guidance Career, dake garin Potiskum da North-East Biotech Services Limited, da Auxiliary International Health Sciences Academy, dake garin Nguru. Sakataren ya bukaci mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan da wuraren da abin ya shafa domin dakile yaudara a fannin kiwon lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: