Gwamnatin Kano ta ware kudi naira biliyan 4 da milyan dari 6 ga jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi

0 162

Gwamnatin jihar Kano ta ware kudi naira biliyan 4 da milyan dari 6 domin ginin ofishin gudanarwa da kuma samar da sauran ababen more rayuwa a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi mallakin gwamnatin jihar.

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Isa Yahaya Bunkure shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai jiya.

Bunkure ya ce tun da aka kafa jami’ar, ta samu tallafin kudi da dama karkashin gwamnatin  Abba Kabir Yusuf. Ya ce tallafin da gwamnatin ke baiwa jami’ar ya samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a makarantar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: