Gwamnatin Najeriya ce ta hana a kama shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji in ji Shugaban Kwamitin Yaki da ‘Yan Ta’adda

0 731

A cewar Sani Shinkafi, wani kwararren masanin tsaro kuma tsohon shugaban kwamitin yaki da ‘yan bindiga a Zamfara, gwamnatin Najeriya ce ta hana a kama shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji.

A wata ganawa da aka yi da shi a Channels TV, Shinkafi ya bayyana cewa a wani farmaki da aka kai da hadin gwiwar CJTF da CPG (Askarawa) a dajin Shinkafi, an kusa kama Turji kuma an kashe daruruwan mayakansa. Sai dai gwamnatin tarayya ta dakatar da farmakin, tana mai cewa za a nemi zaman lafiya da shi ta hanyar tattaunawa a yi sulhu.

Shinkafi ya ce da ba a hana wannan farmaki ba, da yanzu Bello Turji ya zama tarihi. Ya kara da cewa Turji daga baya ya ki amincewa da zaman sulhu

Ya ce, daga cikin dalilan da ke hana nasara akan Turji, akwai rashin hadin kai daga sojoji da jami’an tsaro, karancin kayan aiki da goyon baya ga CJTF, Kauyen da Turji ke buya ba a iya shiga da mota, sannan kuma yawancin CJTF ba ‘yan asalin jihar ba ne, don haka ba su da cikakken sanin yankin.

Gwamnatin jihar Zamfara a halin yanzu ta bayyana cewa ba za ta taba tattaunawa da ‘yan bindiga ba. Kuma har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta fitar da bayani kan wannan batu ba. Haka nan NSA Ribadu ma bai amsa kira ko sakon manema labarai ba kan wannan batun.

Leave a Reply