Gwamnatin Najeriya ta samar wa manoma sabbin iri 49 masu ƙarfin tasiri don gabaka noma

0 164

Kwamatin duba ingancin iri na noma a Najeriya National Varieties Release Committee (NVRC) ya fito da sabbin iri 49 masu ƙarfi don haɓaka harkokin noma a ƙasar.

Shugaban NVRC, Oladosu Awoyemi, shi ne ya sanar da hakan ranar Laraba yayin taronsu karo na 30 inda suka saka wa irin suna da yi musu rajista da kuma sakinsu ga manoma a birnin Ibadan na Jihar Oyo, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mista Awoyemi ya ce rukunin irin 49 na amfanin gona 11, an miƙa su ga hukumar bincike da tantancewa ta Najeriya da kuma cibiyoyin ‘yan kasuwa, inda suka amince da su.

Daga cikin sabbin irin amfanin da aka saka akwai na shinkafa da rogo da alkama da masara.

BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: