‘Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani mutum bisa zargin kashe mijin wacce ake zargin budurwarsa ce.

Abdullahi Sale mai shekara 22 ana zargin ya kashe Muhammad Tukur mai shekara 22, bayan Muhammad Tukur ya zarge shi da soyayya da matarsa.

Kakakin ‘yansanda na jiha, Lawan Shiisu Adam, wanda ya sanar da haka cikin wata sanarwa, yace lamarin ya auku a kauyen Rabadan dake karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.

Yace marigayi Muhammad Tukur ya tunkari Abdullahi Sale bisa zargin soyayya da matarsa, inda ya gargade shi akan ya fita harkar matarsa. A fadan da ya biyo baya, Abdullahi Sale ya jiwa mijin matar rauni da addar da ya kwace a hannunsa.

Kakakin yansandan yace Muhammad Tukur ya mutu a ranar 7 ga watan Janairu a asibitin tarayya na Birnin Kudu inda aka kai shi domin jinyar raunukan da ya samu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: