Rundunar ‘yansandan kasa ta kara wa’adin cike takardar neman shiga aikin dansanda

0 126

Rundunar ‘yansandan kasa ta kara wa’adin cike takardar neman shiga aikin dansanda da ake yi ta internet domin wadanda ke sha’awar shiga aikin a matsayin kurata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan kasa, Frank Mba, cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya yace yanzu sabuwar ranar rufe shafin cikewar ita ce Asabar, 22 ga watan Janairun da muke ciki.

A cewarsa, an kara wa’adin cikewar ne saboda neman masu sha’awa daga yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu su cike guraben da aka ware musu.

Frank Mba ya kara da cewa da wannan karin wa’adin, shafin cikewar ta internet zai cigaba da kasancewa a bude har zuwa karfe 12 na daren sabuwar ranar 22 ga watan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: