Gwamnatin Najeriya tace sai ta kwatowa wani dan kudancin kasar hakkinsa bisa kisan kiyashin da akayi masa a kasar Afirka ta Kudu

0 79

Shugabar hukumar kula da yan Nigeria mazauna kasashen ketare Mrs Abike Dabiri-Erewa a yau tace, zasu gudanar da bincike bisa kisan wani dan Nigeria mai suna Mr Olusola Solarin da akayi a kasar afrika ta kudu a ranar 12 ga watan Disamba na 2021.

Dabiri-Erewa ta bayyana hakan ne a lokacin datake tattaunawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN tace, adadin yan kasar nan da ake kashe a kasar Afrika ta kudu sunkai 127 tindaga 2019 zuwa yanzu.

An kuma gano cewa jamian yan sandan kasar ne suka kashe mutane 13 daga cikin su.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da kungiyyar yan Nigeria mazauna kasar tayi Allah wadai da kisan na kwanan nan.

An gano cewa an kashe Solarin ne a lokacin dayake kokarin kai kayan da yake siyarwa zuwa wajen birnin Johannesburg.

Leave a Reply

%d bloggers like this: